ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin kasar Mauritania sun sanar a safiyar yau Litinin cewa, a daren jiya Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar Mauritania Muhammad Wuld Sheikh Abdullah rasuwa, bayan fama da wata yargajeruwar rashin lafiya a daren na jiya.
Muhammad Wuld Sheikh Abdullah ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, yayin da fadar shugaban kasar ta Mauritania ta sanar makoki na tsawon kwanaki uku, domin alhinin rasuwarsa.
Marigayin dai ya rike mukamai da dama a kasar ta Mauritania tun a cikin shekarun 1970, kamar yadda kuma ya zama shugaban kasar a zaben watan Airilun 2007, inda ya lashe zaben a zagaye na biyu.
Sai bayan shekara 1 da watanni hudu,a cikin watan Agustan shekara ta 2008, tsohon shugaban kasar Muhammad Wuld abdulaziz ya yi masa juyin mulki.
A yau ne dai ake sa ran hukumomin kasar za su fitar da bayani dangane da yadda za a gudanar da janazarsa.
342/